Zuba kudin wannan shiri a cikin kasashe takwas na kungiyar tattalin arziki da kudi ta yammacin Afrika (UEMOA) ya samu amincewa daga kwamitin zartarwa na kungiyar a yayin zaman taro karo na 102 da ya gudana a birnin Ouagadougou na kasar Burkina Faso a gaban idon shugaban BOAD, Christian Adovelande, in ji wata sanarwar bankin.
Biliyan 6 din na Sefa ya kasance wani matakin faro na shirin tabbatar da alfanun makamshin hasken rana (PROVES), wanda ya shafi jimillar Sefa biliyan 80.
Bankin BOAD dake cibiya a birnin Lome na kasar Togo, wata hukuma ce ta kudi ta kasashe guda takwas na kungiyar UEMOA dake kunshe da kasashen Benin, Burkina Faso, Cote d'Ivoire, Guinee Bissau, Mali, Nijar, Senegal da Togo. (Maman Ada)