Da yake tabbatar da hakan a ranar Litinin, ministan wajen kasar Togo Robert Dussey, ya ce za a gudanar da taron ne tsakanin ranekun 10 zuwa 15 ga watan nan, da nufin zakulo hanyoyin magance kalubalen tsaro a tekunan Afirka, da matsalar su ba bisa ka'ida ba, tare da tabbatar da kare nagartar ruwayen nahiyar.
Ana sa ran shuwagabannin nahiyar kimanin 25 zuwa 30 ne za su hallara, cikin jimillar wakilai 3,000 da ake fatan isar su taron.(Saminu Alhassan)