in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gudanar da makon nune-nunen fina-fine tsakanin Sin da Togo a birnin Lome
2016-09-21 13:10:08 cri
An gudanar da makon nune-nunen fina-fine tsakanin Sin da Togo a birnin Lome, hedkwatar kasar Togo a ran 19 ga wata.

Kuma wannan rana ta kasance rana ta cika shekaru 44 da kafuwar dangantakar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu, jakadan kasar Sin dake Togo Mista Liu Yuxi, ministan mai kula da harkokin yada labarai da al'adu, motsa jiki da ba da ilmi Mista Guy Madje Lorenzo, da kuma sauran jakadun kasashe daban-daban dake Togo su fiye da 500 sun halarci wannan gaggarumin biki.

A cikin jawabin da ya bayar, Mista Liu ya nuna cewa, al'adu sun kasance wata gada wajen sada zumunci, kuma ya yi imani da cewa, cimma nasarar gudanar da bikin zai amfana wajen zurfafa zumunci da kuma kara fahimtar juna tsakanin jama'ar kasashen biyu. Sin kuma na fatan karfafa hadin gwiwa tare da kasar Togo don tabbatar da ci gaban da aka samu a yayin taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika a Johnnesburg, da da shawarwarin da aka yi tsakanin shugabannin kasashen biyu. Kana tana fatan zurfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a fannonin al'adu, motsa jiki da nufin kara dankon zumunci tsakanin jama'ar kasashen biyu.

A nasa bangare kuma, Mista Guy Madje Lorenzo ya ce, kasar Togo na farin ciki sosai don gudanar da wannan aiki, kuma yana fatan za a kara gudanar da karin irin wadannan ayyuka nan gaba don kara fahimtai juna da zumunci tsakanin jama'ar kasashen biyu. Baya ga haka ya bayyana cewa, wannan aiki zai sa kaimi ga bunkasuwar sha'anin fina-finai a kasar Togo. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China