in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Lome: Sojoji na kasashe 9 na Afrika na samun horo game da kare fararen hula
2016-08-09 11:34:05 cri

Tun a ranar Litinin ne sojojin kiyaye zaman lafiya na kasashe 9 suka fara halartar shirin ba da horo da ya shafi fasahar sadarwa, da shiga tsakani da kuma ba da kariya ga fararen hula, a cibiyar ba da horo game da ayyukan zaman lafiya da ke Lome na kasar Togo.

Wannan horo ya kasance wani bangare na shirin ba da horo da taimako ga kasashen Afirka wajen gudanar da shirin ko-ta-kwana, wanda hukumar kasar Amurka kan zaman lafiya (AIP) karkashin shugabancin ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurkar ta shirya.

Babbar jami'ar AIP,dokta Illana Lancaster ta bayyana cewar, ma'aikatanta suna aiki ne domin baiwa sojojin wanzar da zaman lafiya dabarun da suka dace.

Wakilin shugaban hafsan sojojin Togo (FAT), Kanal Tchedre Gado ya ce, wannan horo ya shafi neman hanyoyi mafi dacewa don shimfida zaman lafiya, ta yadda za a samu ci-gaba a karshe. (Laouali Souleymane)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China