Gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi kira ga kamfanonin kasa da kasa da ke da alaka da aikin gona, da su agazawa sashen kiwon kifin kasar.
Darektan sashen kiwon kifi na kasar Mu'azu Mohammed shi ne ya yi wannan kiran yayin wani taron kara wa juna sani da aka shirya a Abuja, fadar mulkin kasar.
Ya ce, muddin irin wadannan kamfanoni suka taimaka da kayayyakin noma na zamani, samar da horo ga masu kiwon kifi da samar da abincin kifaye masu inganci, hakan zai taimaka wajen samar da isassun kifaye, zai kuma rage kiyafen da ake shigo da su cikin kasar.
Darektan ya kuma yi kira ga kasashen duniya da su kawo dauki a bangaren bincike, game da abin da ya kira abincin kifaye marasa inganci da ake samarwa a kasar.(Ibrahim)