in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Muhimman labarai daga wasu jaridun Najeriya (161104)
2016-11-04 19:02:53 cri

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya bayyana a jiya Alhamis cewa, yana jin kamar ya bar mulki, saboda abin da ya kira gazawar jihohin kasar 27 cikin 36 na biyan albashin ma'aikata ba tare da wani dalili ba.(The Guardian)

Gwamnatin Najeriya ta ce, tana tsimin dala miliyan 4.5 a ko wace rana sakamakon tsame hannunta daga tallafin albarkatun man fetur.

Karamar ministar kasafin kudi da tsare-tsare ta kasar Zainab Ahmed ce ta shaidawa manema labarai hakan. Tana mai cewa, cire tallafin man da gwamnati ta yi wani bangare ne na tsauraran matakan da fadar shugaban kasar ta bullo da su da nufin farfado da tattalin arzikin kasar.(Vanguard)

A wani labarin kuma, karamar ministar ta ce, a wata mai zuwa ne za a kammala shirin farfado da tattalin arzikin Najeriyar na shekaru uku.

A cewarta, shirin zai yi bayani filla-filla game da manufofin tattalin arziki na gwamnati wadanda za su yi wa masu zuba jari na gida da na ketare jagora.(The Punch)

A jiya Alhamis ne majalisar dattawan Najeriya ta yi watsi da bukatar karamin kasafin kudi na matsakaicin zango(2017-2019) da shugaba Buhari ya gabatar mata, saboda babu komai a cikin kundin.(Daily Trust)(Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China