Kakakin hukumar ta NIMASA Lami Tumaka ta bayyana a cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin kasar Sin na Xinhua ya samu kwafe cewa,an gudanar da kamen ne a ranar Jumma'a kusa da gabar ruwan Legas.
A cewarta, binciken farko-farko ya nuna cewa, mutanen masu kutse ne kawai da suka so bin jirgin zuwa kasar Amurka domin samun rayuwa mai inganci a can.(Ibrahim)