A ranar Litinin da ta gabata ne, hukumar 'yan sandan Najeriya ta sanar da cewa, ta tura 'yan sanda mata kimanin 100 zuwa sansanonin 'yan gudun hijirar, domin su gudanar da bincike. Manufar tura jami'an shi ne, domin tabbatar da tsaron lafiyar dubban mata da kananan yara dake rayuwa a sansanonin.
A makon jiya ne, shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya bada umarnin a gaggauta gudanar da bincike, bayan samun wani rahoto da hukumar kare hakkin dan adama ta fitar, inda ya zargi wasu daga cikin sojoji da 'yan sandan kasar da aikata fyade kan mazauna sansanonin 'yan gudun hijira a kasar. (Ahmad Fagam)