Ministan watsa labarai, al'adu da yawon shakatawa a tarayyar Najeriya Lai Mohammed, ya ce har zuwa yanzu ana ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki, domin ganin an ceto raguwar 'yan matan Chibok su sama da 197, wadanda mayakan kungiyar Boko Haram ke tsare da su, sabanin yadda wasu ke cewa tattaunawar ta balbalce. (The Guardian)
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sha alwashin duba alkaluman farashin man fetur a kasar, a wani mataki na dakile hauhawar farashin na mai. (Vanguard)
Kungiyar kwadago a Najeriya NLC, ta bukaci mahukuntan Najeriya, da su kaucewa daukar duk wani mataki na karin kudin man fetur. (The Punch)