in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun Najeriya sun dakile yunkurin harin kunar bakin wake a arewacin kasar
2016-11-05 12:07:07 cri
Sojojin Najeriya sun yi nasarar dakile hare haren kunar bakin wake har sau biyu, wadanda kungiyar Boko Haram ta shirya kaddamarwa a jahar Borno dake arewa maso gabashin kasar.

Mai magana da yawun rundunar sojin kasar Sani Usman, ya ce da yammacin ranar Jumma'a ne, dakarun Najeriyar suka kashe mayaka 5 a yankunan Yamatake da Gwoza dake jahar Borno.

Sani Usman, ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, cikin 'yan kunar bakin waken da sojojin suka kashe har da mace guda, wacce ta yi yunkurin kutsawa sansanin soji dake yankin Yamatake.

Ya kara da cewa, soja guda ya rasa ransa a lokacin da ake musayar wuta tsakanin dakarun Najeriyar da mayakan na Boko Haram.

Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da rundunonin yaki na musamman a 'yan watannin da suka gabata a yankurin da take na murkushe kungiyar 'yan ta da kayar baya a yankunan jahar Borno dake arewa maso gabashin kasar. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China