Cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na internet, hukumar ta NNPC ta ce, tun daga watan Augusta yawan farsata bututun man kasar ya fara raguwa, idan aka kwatanta wanda aka samu a watan Yuli wanda ya kai kimanin 311.
A halin yanzu, gwamnatin Najeriya tana cigaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki a yankin Niger Delta, domin lalibo bakin zaren cimma yarjejeniyar sulhu da tsagerun yankin don kawo karshen ta'annatin da suke yiwa kayayyakin aikin hakon danyen man kasar.
Ganawa ta baya bayan nan ita ce wanda shugaba Muhammadu Buhari da kansa ya jagoranta, wacce aka fara a ranar Litinin din da ta gabata, tare da shugabannin yankin Niger Delta inda suka gabatar da bukatunsu ga shugaban kasar, wanda suke ganin biyan bukatun zai samar da dawwammman zaman lafiya a yankin.
Matsalar yawaitar farfasa bututan man a yankin, ta haddasa raguwar adadin danyen man da kasar ke samarwa.(Ahmad)