Wadannan ka'idoji uku sun hada da, na farko, ya kamata a daidaita ayyukan da ake yi a fannonin magance matsalar sauyin yanayi da neman fasahohin da abin ya shafa da kuma neman taimakon kudade game da wannan aiki da sauransu a yayin da ake aiwatar da yarjejeniyar Paris. Na biyu, bai kamata a yi watsi da ra'ayin da aka cimma ba. Na uku kuma na karshe, ya kamata a fahimtar da kasashe masu tasowa game da wannan aiki, yayin da ake kokarin taimakawa gwamnatocin kasashen duniya yadda za su karfafa wannan aiki. (Maryam)