in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta ambata nasarorin da ta samu na dashen itatuwa wajen kare muhalli
2016-11-10 09:31:48 cri

Kasar Sin ta yiwa taron COP22 na birnin Marrakesh tsokaci game da irin manyan nasarorin da ta samu a shirinta na dashen itatuwa.

Hukumar kula da tsare tsare ta kasar Sin, ta bayyana wasu daga cikin irin hanyoyi da matakan da kasar ta dauka game da shirin inganta dashen bishiyoyi a matsayin wata sahihiyar hanya ta kare muhalli, tare da samun tallafin asusun kula da gandun daji na kasa da kasa.

Bisa hadin gwiwa da abokan hulda na cikin gida da kuma na kasa da kasa, shirin dashen bishiyoyi na kasar Sin ya cimma nasarori masu yawan gaske, kuma ya samar da dabaru musamman domin tallafawa kasashe maso tasowa.

Shirin ya kasance tamkar wani dandali ne na ma'aikatan kula da dashe bishiyoyi na duniya, inda ake musayar karewa da dabaru, wadanda za su taimaka wajen tinkarar sauyin yanayi, da kuma inganta rayuwar bil adama.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China