Jami'ar ta sanar da hakan ne a taron manema labarai gabanin kaddamar da taron kasashen da suka amince da wannan yarjejeniyar karo na 22 da zai gudana yau a birnin Marrakesh na kasar Morocco.
A watan Disamban shekarar 2015 ne dai aka amince da yarjejeniyar a birnin Paris na kasar Faransa. Kana a watan Oktoba, kasashe 96 da kungiyar tarayyar Turai (EU) suka sanya hannu a kanta, daga bisani kuma ta fara aiki a ranar 4 ga watan Nuwamban wannan shekara.(Ibrahim)