Afrika ta kasance nahiyar da ta fi fama da abubuwan sauyin yanayi a shekarar 2015, a cewar wani rahoton cibiyar kasa da kasa kan haduran sauyin yanayi (Global Climate Risk Index).
A yayin gabatar da rahoton karo na 12 a taron sauyin yanayi a birnin Marrakech na kasar Morocco, mista Sonke Kreft na Germanwatch ya bayyana cewa, kasashe hudu daga cikin kasashe goma mafi fama da sauyin yanayi a bangaren duniya, sun fito daga Afrika. Kuma sun hada da Mozambique, Malawi, Ghana da Madagascar.
Kasashen dake nuna fitar da abubuwa masu gurbata yanayi mafi kankanta su ne kuma kasashen da suka fi fama da abubuwa mafi tsanani na sauyin yanayi, in ji jami'in.
Haka kuma ya bayyana cewa, zafin rana da aka rika samu ya janyo mutuwar mutane da dama a cikin kasashen da suka ci gaba da masu tasowa.
Mutane na fama da rashin kariya da kuma karancin halin kula da bala'u daga indallahi, musammun ma a cikin kasashen da ba su da ci gaba, in ji mista Kreft.
Rahoton ya bayyana cewa, daga shekarar 1996 zuwa shekarar 2015, fiye da mutane dubu 530 sun mutu dalilin abubuwan sauyin yanayi masu tsanani fiye da 11000.
Kasashen da suka fama sosai a tsawon lokaci guda su ne Honduras, Myanmar da Haiti. (Maman Ada)