Kungiyar kare hakkin dan Adam ta MDD (HCHR) ta yaba a baya-bayan nan da matakin da kasar Ghana ta dauka na rattaba hannu kan yarjejeniyar yaki da azabatarwa da wasu nau'o'in azabatarwa ko cin zarafi, rashin imani ko walakantarwa (OPCAT)
Wannan wani muhimmin ci gaba ne wajen yaki da ayyukan azabatarwa, sauran nau'o'in azabatarwa, rashin imani ko walakantawa, in ji Andrea Ori, shugaban reshen HCHR na yammacin Afrika dake birnin Dakar na kasar Senegal, a cikin wata sanarwar cibiyar yada labaru ta MDD dake birnin Accra na Ghana.
"Muna fatan wani misali na Ghana ya zama abin koyi ga sauran kasashen Afrika da ma sauran kasashen duniya," in ji mista Andrea Ori.
Mista Ori ya karfafa gwiwar gwamnatin Ghana da ta yada wannan yarjejeniya bisa daukar matakan da suka wajaba da kafa wasu hanyoyi na 'yancin kasa da horar da alkalai, lauyoyi da ma'aikaitan kotuna kan abubuwan da yarjejeniyar ta kumsa, ta yadda za a iya aiwatar da ita baki daya.
A ranar 23 ga watan Satumba, Ghana ta rattaba hannu kan yarjejeniyar da babban taron MDD ya cimma a shekarar 2002, wadda kuma ta fara aiki a shekarar 2006. Kuma ya kamata yarjejeniyar ta fara aiki kwanaki 30 bayan rattaba hannu kanta. (Maman Ada)