A jiya Litinin hukumarr zaben kasar Ghana (EC) ta soke masu neman tsayawa takarar shugabancin kasar a babban zaben da za'a gudanar a wannan shekara su 13, yayin da ta amince da 'yan takara 4 kacal a matsayin wadanda za su fafata a zaben neman kujerar shugabancin kasar.
'Yan takarar da hukumar ta EC ta amince da su, sun hada da shugaba mai ci John Dramani Mahama na Jam'iyyar NDC, da Nana Addo Dankwa Akufo-Addo na babbar jam'iyyar adawar kasar ta NPP, da Ivor Kobina Greenstreet na Jam'iyyar CPP, sai kuma Jacob Osei Yeboah mai neman takarar a karkashin indifenda.
Shugabar hukumar zaben kasar Ghana Charlotte Osei, ta fadawa taron manema labaru a birnin Accra cewa, haramtawa 'yan takarar shiga zaben shugabancin kasar na wannan shekara ya biyo bayan samunsu da laifukan karya dokokin zaben kasar ne.
Laifukan sun hada da yin magudi wajen rubuta bayanai, da kin ba da cikakkun bayanai da ake bukata, da kuma rashin cike takardun neman shiga zaben yadda ya dace.
Ta kara da cewa, jami'an 'yan sanda za su binciki wasu daga cikin 'yan takarkarin game da yin magudin domin kamawa da kuma hukunta su.(Ahmad Fagam)