Shugaban tawagar wakilan kasar Sin, kana mataimakin shugaban hukumar kula da gandun daji na kasar Sin Liu Dongsheng ya bayyana a yayin bikin cewa, yarjejeniyar, wani muhimmin shirin kiyaye muhallin halittu da kuma tabbatar da ci gaba da yin amfani da su yadda ya kamata. Muddin ana bukatar kyautata harkokin kiyaye da kuma ci gaban aikin, wajibi ne sai kasashen duniya sun gudanar da ayyukan kare namun daji da tsire-tsiren daji yadda ya kamata, da kuma fahimtar da kasa da kasa dangane da kokarin da suka yi a wannan fanni.
Kaza lika, ba za a kawo karshen cinikin namun daji da tsire-tsiren daji ba, sai dai an dauki matakan da suka dace wajen hana saye da sayar da wadannan kayayyaki.
Bugu da kari, babban sakataren yarjejeniyar CITES John Scanlon ya taya kasar Sin murna dangane da manyan sakamakon da ta samu cikin shekaru shida da suka gabata bayan aiwatar da yarjejeniyar yadda ya kamata. Ya kuma nuna cewa, kowa ya ga irin muhimmiyar rawar da kasar Sin ta taka wajen aiwatar da yarjejeniyar CITES, inda kasar ta dauki nagartattun matakai wajen yaki da masu cinikin namun daji da tsire-tsiren daji ba bisa doka ba. A sa'i daya kuma, kasar ta dukufa wajen raya harkokin cinikin namun daji da tsire-tsiren daji bisa doka mai dorewa. (Maryam)