Cikin jawabin sa na bude taron, shugaban hukumar UNEP Achim Steiner ya bayyana cewa, a taron wannan karo, za a mai da hankali kan yadda za a aiwatar da jadawalin neman dauwamammen ci gaba na shekarar 2030 a fannin kiyaye muhalli, da kuma yadda za a iya kyautata muhalli a zaman rayuwar bil Adam, domin kiyaye lafiyar mutane.
Wannan taron kiyaye muhalli na kwanaki biyar da za a yi, zai mai da hankali kan tattauna batutuwan dake shafar gurbatacciyar iska, da cinikin naman daji ba bisa ka'ida ba, da dai sauransu. Har wa yau za a gaggauta aiwatar da sakamakon babban taron sauyin yanayi na Paris. (Maryam)