in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya za ta kafa tarihi a duniya game da dashen bishiyoyi
2016-08-11 10:44:37 cri

Kasar Kenya na kokarin kafa tarihi a duniya, inda ta kuduri aniyar dasa bishiyoyi kimanin miliyan 5 cikin sa'a guda, a watan Nuwambar bana.

Sakatariyar ma'aikatar muhalli da albarkatun kasa Judi Wakhungu ta bayyana cewar, kasar ta dauki wannan mataki ne a matsayin wani yunkuri na yaki da zaizayar kasar da kuma farfado da tekuna da korama domin samun dausayi a kasar.

Wakhungu ta fada a lokacin bikin kaddamar da dashen bishiyoyi na duniya da aka gudanar a Nairobi cewar, a halin yanzu, Kenya ta yi nasarar cimma kashi 2 cikin 100 na samar da dazuka daga cikin kashi 10 da dokokin kasa da kasa suka tanada, amma sakamakon karuwar matsanancin talauci, da yawan karuwar jama'a, al'amura na neman sukurkucewa.

Ta kara da cewar, wannan shiri zai yi matukar tasiri game da tinkarar sauyin yanayi, da yaki da Hamada, da samar da wadaccen ruwa, da samar da abinci, da kuma inganta rayuwar al'umma ta hanyar kyakkyawan yanayin muhallin halittu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China