in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Daraktan hukumar UNDP ya yaba wa ci gaban da Sin ta samu wajen sha'anin kiyaye muhalli
2016-05-28 16:51:37 cri
Daraktan zartaswa na hukumar UNDP Achim Steiner ya bayyana a kwanan baya cewa, a shekaru goma da suka gabata, kasar Sin ta samu ci gaba wajen kiyaye muhalli, da bunkasa tattalin arziki ta hanyar kiyaye muhalli, hakan ya burge shi sosai.

Achim Steiner ya bayyana hakan a yayin taron manema labaru da aka shirya a gun taron kiyaye muhalli na MDD karo na biyu da aka shirya a Nairobi, babban birnin kasar Kenya, inda ya kara da cewa, kasar Sin ta fice sosai wajen kare ra'ayin kiyaye muhalli.

A sa'i guda Achim Steiner ya bayyana cewa, kasar Sin tana gaba a duniya a fannin fasahar makamashi irin na bola jari. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China