Haka kuma, an tattauna yadda za a iya aiwatar da yarjejeniyar Paris da kuma jadawalin neman dauwamammen ci gaba na shekarar 2030.
Bugu da kari, shugaban hukumar UNEP Achim Steiner ya fidda wata sanarwa bayan da aka kammala taron, inda ya bayyana cewa, batun kiyaye muhalli shi ne muhimmin batu ga dukkanin bil-Adam wadanda suke son neman ci gaba, ana fatan za a iya aiwatar da sakamakon babban taron din yadda ya kamata a nan gaba, ta yadda za a iya ba da gudummawa wajen tabbatar da dauwamammen ci gaban kasa da kasa. (Maryam)