in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Sin ya isa birnin St.Petersburg na Rasha
2016-11-07 13:30:03 cri

A jiya ne firaministan kasar Sin Li Keqiang ya isa birnin St.Petersburg na kasar Rasha bisa gayyatar firaministan kasar Dmitry Medvedev, inda zai halarci taron firaministocin kasar Sin da kasar Rasha karo na 21 baya ga ziyarar aiki da zai gudanar a kasar.

Babban jami'in gwamnatin kasar Rasha ne ya tarbi Li Keqing a filin jiragen sama, daga bisani kuma aka shirya wani kasaitaccen bikin maraba da zuwa kasar Rasha.

Ana sa ran a yayin da ya ke ziyarar a kasar Rasha, firaminista Li zai gana da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da kuma takwaransa Dmitry Medvedev. Kana bayan ganawar tasu, za su kuma gana da 'yan jaridu sannan su kalli bikin rattaba hannu kan yarjejeniyoyin hadin gwiwa da dama a tsakanin kasashen biyu. Kaza lika, za su halarci wasu bukukuwan da suka shafi harkokin al'adu.

Li Keqing ya isa birnin St.Petersburg na kasar Rasha ne bayan da ya halarci taron shgabannin kasar Sin da kasashen tsakiya da na gabashin Turai karo na biyar da kuma ziyarar da ya kammala a kasar Latvia. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China