in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakiyar firaministan Sin ta bayyana sakamakon kwamitin hadin gwiwar al'adu na Sin da Rasha
2016-07-05 10:35:03 cri
Jiya Litinin 4 ga wata, mataimakiyar firaministan kasar Sin Liu Yandong da takwaranta na kasar Rasha Olga Golodets sun jagoranci taron kwamitin hadin gwiwar al'adu na Sin da Rasha karo na 17.

A yayin taron, Liu Yandong ta bayyana cewa, kwamitin hadin gwiwar al'adun Sin da Rasha ya kasance wani muhimmin bangare cikin ayyukan hadin gwiwa a tsakanin firaministan Sin da na Rasha, kuma bisa hadin gwiwar kasashen biyu a wannan fanni, sun habaka hadin gwiwar dake tsakaninsu ta fannoni guda 9 da suka hada da ba da ilmi, yin musayar al'adu, kiwon lafiya, yawon shakatawa, kafofin watsa labarai da dai sauransu, lamarin da ya karfafa zumuncin dake tsakanin al'ummomin kasashen biyu sosai.

Haka kuma, ta ce, a halin yanzu, hadin gwiwar al'adu dake tsakanin Sin da Rasha na bunkasuwa cikin yanayi mai kyau sabo da nasarorin da aka samu bisa fannoni hudu, watau da farko ana maraba da yin musayar al'adu ta fannin musamman a ko wace shekara, na biyu shi ne, musayar al'ummomi a tsakanin kasashen biyu dake ci gaba da karuwa, sa'an nan kuma, ana karfafa hadin gwiwa kan inganta ayyukan musamman, a karshe dai, ana ci gaba da habaka tasirin da aka bayar bisa fannoni daban daban.

Bugu da kari, ta ce, bunkasuwar musayar al'adu a tsakanin kasashen biyu ta karfafa zumuncin dake tsakanin al'ummomin Sin da Rasha, yayin da kuma ake kyautata fahimtar juna a tsakaninmu. Sa'an nan, bisa bunkasuwar hadin gwiwar al'adunsu, ana ci gaba da habaka tasiri na wannan fanni zuwa fannoni daban daban, har ma ya karfafa hadin gwiwar al'adu a tsakanin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai gaba daya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China