A gun taron manema labaru da aka shirya a yau Laraba, mista Hong ya bayyana cewa ta'addanci abokin gaba ne ga dukkanin bil'adama. Don haka a koda yaushe Sin ke nuna kiyayyar ta ga kowane irin nau'in aiki na ta'addanci. Har ila yau a matsayin ta na aminiyar hadin gwiwa a duk fannoni kuma bisa manyan tsare tsare, Sin tana goyon bayan Rasha, wajen tabbatar da tsaro, da zaman lafiya a yankunan ta, da ma duk wasu matakai na yaki da ta'addanci da Rashan za ta aiwatar.
Mr. Hong ya ce Sin na fatan karfafa hadin gwiwa tsakaninta da Rasha, da ma dukkanin sauran kasashen duniya a fannin tsaro, da zummar shawo kan barazanar ta'addanci, da kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.(Fatima)