A yayin da suke tattaunawa da juna da yammacin ranar Asabar a nan birnin Beijing, shugabannin biyu sun amince da karfafa kyakkyawar mu'amala da kuma nuna goyon baya ga junansu da bunkasa amincewa da juna dake tsakanin bangarorin biyu.
Da yake nuna yabo game da irin alfanun da tuntubar juna a tsakanin manyan shugabannin kasashen biyu zata haifar ga huldar da ke tsakanin kasashen biyu da ma ci gaban duniya baki daya, Xi ya bayyana cewar bullo da sabbin dabarun inganta hulda tsakanin kasashen biyu da aka yi a shekaru 20 da suka gabata, ya kara bayyana irin tasirin mu'amalar dake tsakanin kasashen biyu.
Shugaba Xi yace bana ta cika shekaru 15 da rattaba hannu kan yarjejeniyar kyakkyawar makwabtaka da yarjejeniyar abokantaka tsakanin kasar Sin da Rasha, kuma wannan abokantaka da hadin kai, zai cigaba da wanzuwa tsakanin karni bayan karni a kasashen biyu.
Kana ya bukaci a cigaba da tattaunawar siyasa da nuna goyon baya tsakanin kasashen biyu.
A halin yanzu shugaba Putin yana ziyarar aiki ne a nan kasar Sin, kuma wannan shine karo na hudu da ya kawo ziyarar kasar Sin tun bayan darewar shugaba Xi Jinping karagar mulkin kasar Sin a shekarar 2013.