Shugaban Sin ya halarci babban taron tunawa da cika shekaru 15 da daddale yarjejeniyar sada zumunci da hadin gwiwa tsakanin Sin da Rasha
A jiya Asabar, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci babban taron tunawa da cika shekaru 15 da daddale yarjejeniyar sada zumunci da hadin gwiwa tsakanin Sin da Rasha tare da takwaransa na Rasha Vladimir Putin a babban dakin taruwar jama'a, inda shugaba Xi ya gabatar da muhimmin jawabi mai taken "Bunkasa dangantaka tsakanin Sin da Rasha domin samar da makoma mai kyau". Cikin jawabin ya nuna cewa, kamata ya yi Sin da Rasha su ci gaba da kokari tare da juna, da samar da makoma mai kyau bisa ga yarjejeniyar da aka kulla, domin raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon mataki. Yana kuma mai fatan cewar, dangantakar zata dore zuwa ga yaya da jikoki, ta yadda za su iya zama cikin yanayi mai zaman lafiya da sada zumunci.(Fatima)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku