Cikin jawabin na sa, Mr. Chang ya ce, ya kamata a yi amfani da hanyoyin siyasa, da na tattalin arziki, da al'adu da kuma diflomasiyya da dai sauran su, domin yaki da ayyukan ta'addanci, tare da kawar da su gaba daya.
Kana, ya ce, gwamnatin kasar Sin na adawa da ko wane irin nau'i na ta'addanci a ko da yaushe, yayin da take tsayawa tsayin daka wajen daukar matakan yaki da ta'addanci bisa tsarin MDD. Ya ce kasar Sin ita ma na fama da kalubalen ta'addanci, inda kungiyar Turkistan ta gabas, ke ci gaba da haddasa tashe-tashen hankula a kasar, lamarin da ke kawo barazana ga tsaron kasar da kuma al'ummomin ta.
Game da hakan ne kuma, kasar Sin ta tsara dokar yaki da ta'addanci, domin gurfanar da wadanda suka aikata wannan laifi gaban kuliya yadda ya kamata. Bugu da kari, kasar Sin tana aiwatar da kudurorin yaki da ta'addanci da MDD ta tsara yadda ya kamata, yayin da kuma ta dukufa wajen ciyar da hadin gwiwar kasa da kasa a wannan fanni gaba, inda kasar ta kuma ba da gudummawa sosai wajen kiyaye tsaro, da zaman karko a yankin.
An gudanar da taron tsaron kasa da kasa na wannan karo bisa jagorancin hukumar tsaron kasar Rasha, inda ministocin tsaron kasashen Pakistan, da Belarus da sauransu bisa jimilla 18 suka halarci taron. Kana wasu wakilai da masana na MDD, da kungiyar tsaron Turai da sauransu, su ma suka aike da wakilai. (Maryam)