in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Sin da takwaransa na Rasha sun gana da 'yan jarida
2015-12-18 10:17:57 cri

 

A ran 17 ga wata da yamma, firaministan kasar Sin Li Keqiang da takwaran aikinsa na kasar Rasha Dmitri Medvedev sun gana da 'yan jarida a babban dakin taron jama'a dake birnin Beijing na kasar Sin, bayan da suka kammala taron firaministocin kasar Sin da kasar Rasha karo na 20.

A yayin ganawarsu da 'yan jarida, Li Keqiang ya gabatar da sakamakon ganawar firaministocin kasashen biyu, inda ya bayyana cewa, a halin yanzu, yanayin farfadowar tattalin arzikin duniya ba ya da kyau, adadin cinikayyar dake tsakanin Sin da Rasha ya ragu, amma hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu a fannonin makamashi, fasahohin zamani da kuma ciniki ta intanet da dai sauransu ya karu, lamarin da ya haifar da sabon yanayi ga bunkasuwar cinikayya a tsakanin kasashen biyu.

Bugu da kari, Li Keqiang ya ce, ba kawai za a iya tallafa wa jama'ar kasashen biyu ta hanyar karfafa hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Rasha ba, haka kuma, za a iya karfafa aniyar kasashen da tattalin arizkinsu ke saurin karuwa da kasashe masu tasowa wajen farfado da tattalin arzikinsu, wanda zai ba da gudummawa ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya da kuma tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a shiyya-shiyya, har ma a duk fadin duniya baki daya.

A nasa tsokaci, Dmitri Medvedev ya ce, kasarsa na son hada kai tare da kasar Sin domin habaka hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu a fannoni da kuma ta hanyoyi daban daban, ta yadda za a kyautata huldar dake tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China