in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IPU ta yi kira ga masu ruwa da tsaki da su cimma shirin dindindin na daidaita rikicin Syria
2016-10-27 10:17:41 cri
Taron kungiyar majalisun dokoki na kasa da kasa, wato IPU da ke gudana a birnin Switzerland ya zartas da wani kuduri a jiya Laraba, inda ya yi kira ga kasashen Amurka da Rasha da ma sauran bangarori masu ruwa da tsaki da su fito da wani shirin dindindin na kawo karshen rikicin Syria.

Kudurin ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da su tsagaita bude wuta, don tabbatar da tsaro da kuma ba da dama ga masu samar da agajin jin kai ta yadda za su samu saukin isa ga wadanda ke matukar bukatar taimako. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China