Wani labarin na daban wanda kamfanin dillancin labaran Syria ya fitar, ya nuna cewa, dakaru masu adawa da gwamnati sun ci gaba da ruwan boma-bomai kan yankin dake karkashin ikon gwamnatin Aleppo, wanda hakan ya haddasa rasuwar mutane biyu, tare kuma da raunata mutane fiye da goma.
A watan Satumbar bana, sojojin gwamnatin Syria sun samu ci gaba a matakan soja da suke dauka, inda kuma suka yiwa yankunan dake gabashin Allepo kawanya, yanki da yanzu haka ke karkashin ikon 'yan adawar gwamnatin kasar.
Daga ranar 20 zuwa 22 ga wata, sojojin gwamnatin Syria sun tsagaita bude wuta na jin kai tsawon kwanaki 3 a birnin Aleppo. Sai dai bayan hakan rikici ya sake barkewa tsakanin sojojin gwamnati da dakarun 'yan adawar.
Kaza lika a ranar 28 ga watan nan, dakaru masu adawar sun kai babban farmaki kan yankunan dake gabashin Aleppo, wadanda ke mallakar gwamnatin wurin, da nufin tarwatsa gungun sojojin gwamnatin wurin da suka yi musu kawanya. (Bilkisu)