Dattawan Niger Delta sun kara gabatarwa Najeriya wasu karin bukatu
Kwana daya bayan tattaunawar da dattawan yankin Niger Delta suka yi da shugaba Buhari na Najerya, kan yadda za a magance matsalar yankin, sai ga shi kuma a jiya Laraba, sun kara gabatar da wasu jerin bukatu biyar bayan guda tara da suka gabatar tun farko. Matakin da dattawan suka ce zai haifar da mai-ido a tattaunawar warware matsalar yankin da bangarorin biyu ke yi a cewar jaridar Vangurad. (Ibrahim Yaya)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku