Dattawa daga yankin Niger Delta sun tattauna da gwamnati kan yadda za a magance matsalolin yankin
Bisa labarin da jaridar Punch ta bayar, an ce, masu ruwa da tsaki daga yankin Niger Delta karkashin dandalin nan na Pan Niger Delta Forum, sun danganta sabbin hare-haren da ake kaddamarwa a yankin kan abin da suka kira mayar da su saniyar ware da kuma rashin wani ci gaba mai ma'ana a yanki.
Sun kuma bayyana cewa, sun tattauna sosai inda suka fito da shawarwari guda 16 wadanda za su taimakawa gwamnatin tarayya kan yadda za ta cimma nasarar matakan da ta tsara. (Ibrahim Yaya)