in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi kira ga mahukuntan Zambia da su kara azama wajen yaki da cin hanci
2016-11-02 10:54:43 cri

Masu rajin kawo sauyi a kasar Zambia sun ja hankalin mahukuntan kasar da su dauki matakai na zahiri, wajen yaki da mummunar dabi'ar nan ta cin hanci da rashawa, maimakon yawaita alkawura marasa tabbas.

Kiraye-kirayen na baya-bayan nan dai na zuwa ne bayan da shugaban kasar Edgar Lungu, ya bayyana damuwa game da rahotannin da ya samu, masu kunshe da zargin wasu ministocinsa da aikata cin hanci da rashawa. Tuni dai shugaba Lungu ya yi barazanar korar ministocin, muddin aka tabbatar sun aikata laifukan da ake zarginsu.

Da yake tsokaci game da wannan batu, kakakin gungun kungiyoyi masu rajin kare dimokuradiyya ko FDD a kasar Zambia Antonio Mwanza, ya ce abun da suke fatan gani, shi ne gwamnatin ta dauki matakin hukunta ministocin da ake zargi da aikata laifukan cin hanci. Ya ce, sashen binciken laifuka ya gama nasa aiki, sai dai maimakon hukunta masu laifin, shugaban kasar ya maida hankali ga furta kalamai masu kama da kurari kadai.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China