in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manzon musamman na shugaban kasar Sin ya halarci bikin rantsar da shugaban kasar Zambiya
2016-09-14 10:09:25 cri
A jiya Talata ne, Mista Ma Biao manzon musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci bikin rantsar da shugaban kasar Zambiya Edgar Lungu da aka yi a birnin Lusaka hedkwatar kasar, kuma kafin bikin, sai da shugaba Lungu ya gana da Ma Biao a fadarsa.

Yayin ganawar tasu, Mista Ma Biao ya isar da gasuwa da kyakkyawar fatan shugaba Xi Jinping zuwa ga shugaba Lungu. Mista Ma ya ce, Sin na dora babban muhimmanci kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, ya kara da cewa, yanzu ana kokarin tabbatar da matsaya daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma da kuma sakamakon da aka samu yayin taron kolin dandalin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika na Johannesberg, kuma yana fatan ganin an yi amfani da wannan zarafi mai yakini don ciyar da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu gaba.

A nasa jawabin, shugaba Lungu ya nuna godiya kan yadda Mista Ma Biao ya halarci bikin rantsuwar, kuma ya bukaci Mista Ma da ya isar da gaisuwa da godiyarsa ga shugaban Xi Jinping. Shugaba Lungu ya ce, Sin da Zambiya sun kulla zumuncin da ke tsakaninsu ne bisa tushen mutunta juna, fahimar juna da samun moriya juna. A kullum Zambiya tana daukar kasar Sin a matsayin sahihiyar kawa, kuma tana fatan kara hadin gwiwa da kasar Sin don zurfafa hadin gwiwa tsakaninsu a dukkanin fannoni.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China