A cikin jawabinsa na kama aiki, Mista Lungu ya ce, a cikin shekaru biyar masu zuwa, Zambiya za ta ba da muhimmanci wajen kyautata tsarin tattalin arzikinta wanda ya dogaro da sha'anin hako tagulla, ta yadda za a bunkasa sha'anoni iri daban-daban da kara karfin bunkasa sha'anin noma, har ma da karawa kamfanoni masu zaman kansu kwarin gwiwa, da ci gaba da bunkasa muhimman ababen more rayuwa. Ban da wannnan kuma, kasar za ta kara karfin raya sha'anin makamashi da zuba jari da aikin kirkire-kirkire da kimiyya da fasaha da kuma mai da hankali kan kiyaye muhalli da dai sauransu. (Amina)