in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Zambiya ya gargadi masu tada husuma a zaben kasar
2016-02-16 10:27:30 cri
Shugaban kasar Zambiya Edgar Lungu, a Litinin din data gabata yayi fada cewar bazai lamunci duk wani yunkurin tada tarzoma daga bangarorin jam'iyyun siyasar kasar ba, a yayin da ake shirye shiryen gudanar da babban zaben kasar a watan Augustan wannan shekara.

Shugaban yayi wannan gargadi ne bayan wani tashin hankali da bangaren 'yan adawa suka haddasa a gundumar Itezhi-tezhi dake kudancin kasar, shugaban yace ba zai lamunci duk wani yunkurin tada hankali ba a yayin tunkarar babban zaben kasar, har ma ya umarci jami'an 'yan sandan kasar dasu sanya ido don tabbatar da tsaro.

A ranar Asabar din data gabata ne, wasu da ake zargin magoya bayan jam'iyyar adawa ta UPND ne, suka yi kwantan bauna kan tawagar magoya bayan shugaban kasar a yayin da suke kan hanyar su ta dawowa daga gangamin yakin neman zabe.

Maharan sun lalata motocin gwamnati 3, sannan sun jikkata jami'an 'yan sanda biyu.

Su dai 'yan adawar, wadanda ke dauke da makamai sun datse hanyar da magoya bayan shugaba Lungu ke bi, inda suka dinga jifan su da duwatsu, sannan sun yi garkuwa da wasu mutanen kafin daga bisani 'yan sanda su kwato su.

Shugaban na Zambiya ya sha alwashin daukar tsauraran matakai wajen murkushe tarzomar siyasar, a yayin da kasar ke shirin gudanar da zabukan a ranar 11 ga watan Augastan wannnan shekara.

Sanarwar tace, shugaban na Zambiya ya bayyana cewar abin da ya fi lura da shi shi ne samun zaman lafiya a kasar ba wai sakamakon zaben kasar ba, don haka ya kuduri aniyar magance tashin hankali a kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China