in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An jinjina ma shugaban kasar Zambiya a shirin da yake na saka mace ta zama mataimakiyar shi
2016-02-23 09:24:09 cri
Kungiyoyin mata a kasar Zambiya sun yaba ma shugaba Edgar Lungu a kan tabbacin da ya bayar na nada mace a matsayin mataimakiyar shi gabannin babban zaben da ke tafe a wannan shekarar, kamar yadda kafofin watsa labaran kasar suka ruwaito.

A ranar Asabar din da ya gabata ne dai shugaba na Zambiya ya ce mataimakiyar shi a babban zaben da zai gudana a ranar 11 ga watan Agustan wannna shekarar za ta kasance mace saboda shi yana goyon bayan daidaicin jinsi kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.

Cancantar samun mataimaki na daga cikin sabbin gyara da aka yi a kundin tsarin mulkin kasar.

Babbar shugabar wata kungiyar mata na ZNWL Madam Beauty Katebe ta ce ba shakka shugaban kasar yana kara jaddada dadaito a 'yanci kamar yadda aka ganin wajen nada mata a mukaman da za su fadi a ji. Don haka mata na farin ciki kwarai na sani tare da tabbacin da ya ba su cewar zai nada 'yar uwar su a matsayin mataimakiyar shi.

Madam Beauty Katebe ta ce wannan ya kara ma mata karfi wajen kira ga samar da 'yancin mata saboda sun samu shugaban dake mara musu baya. Ta ce nada mace a matsayin mataimakiya har ila yau zai inganta karban mata a manyan mukamai, wanda zai bude hanya ga sauran mata sun cimma matsayi babba a bangaren shugaban shi. (Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China