An bayyana shugaba Lungu, a matsayin wanda ya sake yin nasarar lashe zaben shugaban kasar a ranar 11 ga wannan wata da muke ciki, sai dai Hakainde Hichilema wanda ya yi wa babbar jam'iyyar adawar kasar UPND takara, ya kalubalanci sakamakon zaben a gaban kotu.
Sakataren gwamnatin kasar Ronald Msiska ya sanar da dakatar da shirye shiryen bikin rantsar da shugaban kasar, wanda ake shirin gudanarwa a babban dandalin taron na kasar, sai dai jam'iyyar adawar ta kalubalanci zaben a ranar Juma'ar da ta gabata.
Da farko an shirya rantsar da Mista Lungu ne a Talata mai zuwa.
Kafafen yada labarun kasar sun rawaito cewar, an ga ma'aikata na kwashe kayayyakin aikin bikin rantsuwar bayan samun umarni na dakatar da bikin.
A bisa kundin tsarin mulkin kasar, ba'a rantsar da shugaban kasa matukar an kalubalanci sakamakon zaben kasar. (Ahamd Fagam)