in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zambiya ya gudanar da zabuka cikin zaman lafiya tare da wani babban adadin halartar jama'a
2016-08-12 10:31:57 cri
Hukumar zaben kasar zambiya da masu sanya ido kan zabuka na kasa da kasa sun bayyana gamsuwarsu kan yadda zabuka suka gudana cikin kwanciyar hankali da lumana da kuma yadda jama'ar kasar suka halarci zabukan sosai.

Priscilla Isaac, shugabar hukumar zaben Zambiya (ECZ) ta bayyana cewa rahotonnin da aka samu daga bangarori daban daban na kasar sun nuna babban adadin halartar jama'a.

Baya ga zaben shugaban kasa, masu zabe na kada kuri'u domin zaben 'yan majalisu 156 da magajin gari 1624 da kuma mashawarta, haka kuma da yanke shawara ta hanyar zaben jin ra'ayin jama'a kan wani kuduri na sashen uku na kundin tsarin mulki, dake shafar 'yancin jama'a. Game da zaben shugaban kasa, an fafata tsakanin Edgar Lungu da Hakainde Hichilema.

Shugaban 'yan adawa ya jefa kuri'arsa a rumfar zaben dake makarantar sakandaren Kabulonga, dake Lusaka, babban birnin kasar, tare da bayyana cewa 'yan Zambiya na fatan zabuka cikin 'yanci, kuma na gaskiya da adalci. A cewarsa, mutumin da ya lashe zabuka ba zai kasance ba da muhimmanci idan har zabuka ba a gudanar da su ba cikin 'yanci da adalci.

Mista Lungu, ya yi nasa zaben a cocin John Howard dake cikin babban ginin Chawama, ya kuma bayyana mamakinsa kan yadda mutane suka halarci zabuka, tare da yin kira ga masu ruwa da tsaki da su taimakawa hukumar zabe wajen gudanar da aikinta yadda ya kamata. Za'a fitar da sakamakon dindindin na zaben shugaban kasa a ranar Asabar da yamma. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China