Ministan tsaron kasar Amurka Ashton Baldwin Carter ya bayyana jiya Talata a birnin Paris cewa, kawancen sojojin da ke yaki da 'yan tawayen IS sun killace birnin Reqqa da ke arewacin kasar Syria, amma duk da haka da wuya a kai hari a birnin yanzu.
Shi ma babban sakataren kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg ya ce, kungiyar NATO ta bukaci jiragen saman kawancen da su hattara. (Tasallah Yuan)