in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi kira da a kara taimakon da za a baiwa kasashe masu karbar 'yan gudun hijirar Syria
2016-10-25 14:03:44 cri
Babban jami'i mai kula da harkokin 'yan gudun hijira na MDD Filippo Grandi, ya yi kira ga gamayyar kasa da kasa da su kara ba da taimako ga kasashe masu karbar 'yan gudun hijirar kasar Syria.

Mr. Grandi ya ce, ya zuwa yanzu, bisa jimilla yawan 'yan gudun hijirar kasar Syria dubu 24 sun bar kasar Jordan, inda suke shiga kasar Amurka da wasu kasashen Turai, kana a nan gaba, kimanin 'yan gudun hijirar Syria dubu 50 ne ake hasashen za su bar kasar ta Jordan.

Bisa hakan ne kuma Grandi, ya yi kira ga gamayyar kasa da kasa da su shirya, domin fuskantar 'yan gudun hijira masu dimbin yawa, sakamakon yakin da ake fafatawa a birnin Mosul na kasar Iraqi. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China