in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afirka ta Kudu: Dokar hakar ma'adanai za ta haifar da rashin tabbas, in ji 'yan adawa
2016-11-02 10:17:00 cri

Wakilan jam'iyyar DA mai adawa a kasar Afirka ta Kudu, sun ce dokar hakar ma'adanai da aka yi wa gyaren fuska, za ta haifar da rashin tabbas, duba da yadda ta tanaji bai wa ma'aikatar hakar ma'adanan kasar karin iko na sarrafa harkokin hakar ma'adanai.

Tuni dai 'yan majalissun dokokin kasar 198 suka jefa kuri'un amincewa da dokar mai lakabin MPRDA, yayin da kuma masu adawa da ita su 81 suka jefa kuri'un rashin amincewa, kana dan majalissar daya ya kaurace wa kuri'ar.

Karkashin tanajin dokar dai gwamnatin tarayyar kasar na da kaso 20 bisa dari na ribar ma'adanan da ake hakowa a kasar, baya ga tanajin sarrafa wani kaso na ma'adanan a cikin gida, maimakon fitar da shi waje kafin sarrafawa. Har wa yau gwamnatin kasar na da ikon sayen wani karin kaso na ma'adanan a farashi madaidaici.

An dai mika wannan doka ga hukumar dake lura da harkokin lardunan kasar domin neman amincewar ta, a gabar da masu adawa da ita ke cewa, amfani da ita, ka iya haifar da yaduwar cin hanci da rashawa, duba da cewa, ta tanaji damar da manyan jami'an ma'aikatar ma'adanan kasar za su yi amfani da ita, wajen azurta kan su da sauran wadanda suke kauna.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China