Stephane Dujarric, ya shedawa 'yan jaridu a jiya Juma'a cewa, kimanin mutane miliyan daya da dubu 800 ne rikici ya tilastawa ficewa daga gidajensu, kana mutane miliyan 4 da dubu 400 ne ke cikin matsananciyar bukatar agajin gaggawa, sannan sama da yara dubu 400 ne ke fama da matsalar karancin abinci mai gina jiki.
Dujarric ya ce, hukumomin agaji na MDD suna cigaba da fuskantar kalubale wajen gudanar da ayyukansu, kasancewar basu da damar shiga dukkannin yankuna na shiyyar arewa maso gabashin Najeriyar, don haka akwai matukar wahala ga jami'an bada agajin da ake dasu a halin yanzu, su samu damar isa yankunan da mutanen dake cikin bukatar gaggawa ke zaune.
Ya kara da cewa, hukumar ta UNICEF tana fama da matsalar kudaden gudanarwa, kasancewa kashi 25 cikin 100 kadai na kudaden gudanar da ayyukanta na shekarar 2016 a kasar ta samu, yayin da a daya bangaren, shirin samar da abinci na MDD (WFP) yana bukatar dala miliyan 30 domin cigaba da gudanar da ayyukansa cikin watanni 6 masu zuwa.(Ahmad Fagam)