A jiya Talata majalisar dattijan Najeriya ta kada kuri'ar kin amincewa da bukatar da shugaban kasar Muhammad Buhari ya gabatar mata, na neman amincewarta don ciyo bashin dalar Amurka biliyan 29.9 daga bankin duniya.
A makon da ya gabata ne, shugaba Buhari ya aike wa majalisar bukatarsa ta neman rancen kudaden daga bankin duniya.
Da ma dai tuni shugaban na Najeriya ya bayyana dalilansa na ciyo bashin kudin, inda yake da muradin amfani da su wajen gudanar da ayyukan ci gaban kasar daga dukkan fannoni.
Tun lokacin da shugaban majalisar dattijan kasar ya gabatar da bukatar a zauren majalisar, mambobin majalisar suka sa kafa suka shure bukatar nemo rancen ba tare da yin muhawara kan bukatar shugaban kasar ba.
Sau biyu shugaban majalisar dattijan Bukola Saraki yana nanata bukatar a zauren majalisar amma sanatocin suka juya baya kan bukatar.
Yan majalisar dattijan sun bayyana dalilansu cewar, al'ummar Najeriya suna kyamar ciyo bashin daga ketare, inda suke ganin matakin zai iya kuntatawa kasar, hakan ne tasa suka bijiriwa wannan bukata. (Ahmad)