in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Muhimman labarai daga wasu kafofin watsa labaran Najeriya
2016-10-28 19:01:52 cri
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, zai gana da masu ruwa da tsaki a yankin Niger Delta mai arzikin mai a ranar Talata, a wani mataki na kawo karshen lalata kayayyakin hakar mai da tsagerun yankin ke aikatawa.

Rahotanni dai na cewa an dakatar da bangarori da dama na ayyukan hakar danyen mai a yankin, sakamakon fasa bututan mai da na iskar gasa da tsagerun yankin na Niger Delta ke yi. (Daily Trust)

Dakarun rundunar da aka dorawa alhakin dakile ayyukan bata-gari mai lakabin "Operation Delta Safe", sun ce sun gano wasu kasusuwa na gawawwakin mutane 23, a yayin wani sumame da suka gudanar a maboyar wasu 'yan tada-kayar-baya da ake zargin 'yan kungiyar "Bakassi Strike Force" ne. An dai samu sassan kasusuwan ne a yankin kananan hukumomin Bakassi da Akpabuyo dake jihar Cross River. (The Punch)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China