Da alamun kamfanin kera motoci na Ford da ke kasar Amurka ya dakatar da shirinsa na tura rukunin motoci 500 kasuwannin Najeriya, sakamakon matsalar tattalin arzikin da kasar ta ke fuskanta.
Rahotanni na cewa, kamfanin ya hada wadannan motoci a reshensa da ke kasar Afirka ta Kudu, kuma an kammala dukkan shirye-shiryen da suka wajaba na tura motocin zuwa Najeriya kafin ya yanke wannan shawara.(The Punch)
Tsagerun Niger Delta sun yi ikararin cewa, su ne suka kai harin ranar Lahadi kan bututun iskar gas a yankin, domin nuna adawa da tattaunawar da za a yi tsakanin mahukuntan kasar da shugabannin yankin mai arzkin mai da ke yankin kudancin kasar.
Wata sanarwa da kungiyar 'yan tawayen mai suna Niger Delta Greenland justice Mandate ta rabawa manema labarai, ta ce ba za ta goyi bayan tattaunawar da shugaba Muhammadu Buhari zai yi da wakilan daga yankin da nufin kawo karshen fasa batutan man da 'yan tawayen ke yi a yankin ba.(The Guardian)