Mutane tara sun mutu a ranar Talata a cikin fashewar wata mota a Maiduguri, babban birnin jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya, in ji 'yan sandan wurin.
Motar ta fashe a kusa da wata tashar binciken jami'an tsaro dake kan hanyar Gubio, in ji Victor Isuku, kakakin 'yan sandan jihar Borno.
Ana dai zargin kungiyar ta'addanci ta Boko Haram da tada wannan fashewar. Bisa binciken farko da aka gudanar, kakakin 'yan sandan ya bayyana cewa, wata motar Van, dake dauke da mutane guda tara, ta fita daga wata hanyarta sannan ta kama hanyar zuwa garin Gulio a lokacin da ta yi bindiga. Haka kakakin ya kara da cewa, sauran sakamakon binciken za a gabatar da su ga jama'a a nan gaba. (Maman Ada)