Hedkwatar tsaron kasar Najeriya ta ce, dakarun kasar sun yi nasarar ceton mata da kananan yara kimanin 38 daga hannun mayakan Boko Haram a jahar Borno dake arewa maso gabshin kasar.
A wata sanarwar da kakakin rundunar sojin Najeriyar Sani Usman ya sanya wa hannu ya ce, sojojin sun kama wasu mayakan na Boko Haram 6, sannan sun jikkata wasu da dama a lokacin da suke musayar wuta da mayakan a kauyen Dumba dake jahar Borno.
Sanarwar ta ce, matan da aka kubutar da su 19 ne, sannan kananan yaran ma 19.
Sanarwar ta kara da cewa, dakarun runduna ta 8 ta musamman ta sojin kasar sun fara gudanar da aikinsu, inda suka lashi takobin tarwatsa maboyar mayakan Boko Haram a yankunan karkara dake jahar Borno a kusa da kan iyakar Najeriya da Nijer.(Ahmad)