A jiya Alhamis aka gudanar da bikin shigar da al'adun kasar Sin makarantun Najeriya na shekarar 2016 a makarantar midil dake unguwar Garki Abuja, babban birnin kasar. Karamin jakada mai kula da harkokin al'adu na kasar Sin dake Najeriya Yan Xiangdong, da jami'i mai kula da harkokin tarbiyya na yankin Abuja Musa Maikasuwa Yakubu, da kuma darektan kwamitin tarbiyya na yankin Abuja Adamu Noma, tare da malamai da dalibai kimanin 300 daga makarantun yankin 16 sun halarci bikin.
Mr. Yan Xiangdong, ya yi jawabi inda ya bayyana cewa, bikin zai ingiza bunkasuwar al'adu da tarbiyya dake makarantun firamare da midil na Najeriya, ofishin jakadancin Sin dake kasar zai ci gaba da goyon bayan bunkasuwar harkokin tarbiyya a babban birnin kasar, da ba da da karin damammakin samun ilmi ga dalibai.
Musa Maikasuwa Yakubu, ya bayyana cewa, bikin ya samar da wani dandalin musayar ra'ayi kan al'adu ga daliban makarantun firamare da midil na yankin Abuja. Kasar Sin da Najeriya muhimman kasashe ne a fannin raya al'adu, musayar ra'ayi a fannin al'adu zai zurfafa zumuncin dake tsakaninsu.
A gun bikin, ofishin jakadancin Sin ya samar da litattafai da na'urorin DVD da kuma telabijin da dai sauransu ga makarantu 16 na yankin Abuja.(Lami)